An kama matashi mai shekara 23 da ake zargin ya ci zarafin wa wani yaro ɗan shekara goma

0 122

Jami’an ƴan sandan jihar Bauchi da ke aiki ƙarƙashin rundunar maido da zaman lafiya sun kama matashi mai shekara 23 da ake zargin ya ci zarafin wa wani yaro ɗan shekara goma.

Matashin da ake zargi ya yaudari yaron da naira 30 da alawa inda ya nemi yaron ya raka shi wani kango da ke bayan wani gidan mai, a kan titin Kofar Ran domin ya yi bahaya.

Sanarwar da kakakin rundunar ƴan sandan Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar ta ce bayan ya yi bahayar ne kuma, matashin ya buƙaci yaron da ya tuɓe wandonsa ya duba ko ya yi tsarki.

A cewar sanarwar, bayan da yaron ya cire wandonsa ne kuma, matashin ya cakumo yaron ta baya inda ci zarafinsa. Rundunar ta ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa matashin da ake zargi ya fito daga ƙauyen Jingino da ke ƙaramar hukumar Gwaram a jihar Jigawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: