An kama mutane 26 bisa zargin laifukan satar waya, satar babura da karya shaguna

0 171

Rundunar yan sandan jihar Jigawa tace ta kama mutane 26 bisa zargin laifukan satar waya, satar babura, karya shaguna da dillancin miyagun kwayoyi a sassan jihar daban-daban.

Kakakin rundunar DSP Lawan Shiisu Adam wanda ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar, yace sun gano babura 2, da kwamfutoci 6, da na’urorin AC, da wayoyin hannu da miyagun kwayoyi da raguna da sauran kayyaki daga wadanda ake zargi.

Kakakin ya bayyana cewa, wani mai suna Yakubu Usman a unguwar Gandun sarki a Hadejia ya kai rahotan an sace masa babur, daga karshe jami’an yan sanda sunyi nasarar gano babur din a hannun wani Abdullahi Muhammad Walawa, wanda yayi ikirarin yana da makullin gama gari.

A cewar kakakin tsakanin ranakun 17 zuwa 21 ga watannan jami’an yan sanda yankunan Kiyawa, Bamaina da Maigatari sun gano maboyar bata gari bayan samun bayanan sirri, yayin wani sumame da suka kaddamar, sun yi nasarar kama mutane 22 tare da kwato haramtattun kayayyakin sata da na laifi. DSP Lawan Shiisu yace zasu gurfanar da dukkan wadanda ake zargi gaban sharia da zarar sun kammala bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: