Gwamnatin jihar Sokoto ta karbi mutane 66 daga hannun masu garkuwa da mutane a jihar

0 146

Gwamnatin jihar Sokoto ta karbi mutane 66 da dakarun rundunar Operation Hadarin Daji suka kubutar daga hannun masu garkuwa da mutane a jihar.

Sawaba radio ta bayar da labarin yadda hadakar dakarun rundunar suka yi nasarar kubutar da mutane 52 da aka yi garkuwa dasu a karamar hakumar Isa dake jihar Sokoto.

Da yake jawabi yayin mika wadanda lamarin ya shafa kwamadan runduna ta 8 na sojin Najeriya, birgediya janar Alex Tawasimi, yace dakarun sun gudanar da wani samame ta kasa wanda ya kai ga ceto mutanen aka kai Dajin Gundami, bayan watanni 3 da sace su.

Gwamnan jihar ya tabbatar da yunkurin gwamnatinsa na tallafawa jami’an tsaro domin aikin dawo da zaman lafiya da kwaciyar hankali a jihar. Haka kuma gwamnan tare da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko sun bayar da Naira miliyan 16.6 ga mutane 66 da sojoji suka kubutar daga hannun masu garkuwa a tsakanin ranar alhamis zuwa asabat.

Leave a Reply

%d bloggers like this: