Wani hari da Isra’ila ta kai sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Maghazi ya kashe mutane akalla 70

0 230

Ma’aikatar lafiya ta Gaza karkashin Hamas ta ce wani hari da Isra’ila ta kai ta sama ya kashe mutane akalla 70 a sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Maghazi da ke tsakiyar yankin.

Kakakin ya ce akwai yiyuwar adadin wadanda suka mutu ya karu idan aka yi la’akari da yawan iyalai da ke zaune a yankin.

Sojojin Isra’ila sun shaida wa BBC cewa suna duba rahotannin harin.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kafafen yada labaran Isra’ila da na Larabawa suka ce Masar da ke kan iyaka da zirin Gaza ta gabatar da wata sabuwar shawara ta tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Hamas.

A cewar mai magana da yawun ma’aikatar Ashraf al-Qudra, an lalata wani katafaren gida mai yawan jama’a.

A cewar ma’aikatar lafiya, fiye da mutane 20,000 ne aka kashe – akasari yara da mata – yayin da wasu 54,000 suka jikkata a Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba, lokacin da Hamas da wasu kungiyoyin Falasdinawa suka kai hari kan Isra’ila, inda suka kashe mutane 1,200 tare dayin garkuwa da kusan 240. Sojojin Isra’ila sun ce an kashe sojoji fiye da goma a Gaza tun daga ranar Juma’a, wanda ya kawo jimillar hare-haren kasa da aka kaddamar bayan 7 ga Oktoba zuwa 156.

Leave a Reply

%d bloggers like this: