Ma’aikatan gwamnatin tarayya na kokawa kan jinkirin biyan albashin watan Disamba

0 187

Ma’aikatan gwamnatin tarayya a fadin kasar nan na kokawa kan jinkirin biyan albashin watan Disambar 2023.

Sun bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki kasancewar sun gudanar da bikin Kirsimeti a jiya ba tare da kudi ba, yanayin da ya shafi iyalansu, musamman wadanda ba su da wani kudi da suka yi tanadinsa.

Da yawa daga cikin wadanda suka zanta da jaridar Punch sun koka kan yadda ba su yi bikin Kirsimati kamar yadda suka saba gudanar da shagali ba, da girke-girke, gami da ziyarar yan uwa   da abokan arziki.

Bincike ya nuna cewa daukacin ma’aikatan da ke ma’aikatun gwamnatin tarayya da wasu na ofishin shugaban ma’aikatan tarayya da kuma wasu da ke ofishin sakataren gwamnatin tarayya sun bayyana lamarin a matsayin bazata.

An gano cewa lamarin haka yake a jami’o’in gwamnatin tarayya da na polytechnics da kwalejojin ilimi da sauran cibiyoyin gwamnatin tarayya a duk fadin kasar nan. Majiyoyi sun ce ma’aikatan dake aiki a hukumomin samar da kudaden shiga kamar NNPC, da CBN, da dai sauransu ne kawai suka samu albashin watan Disamba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: