An kama mutane 39 da ake zargi da aikata ta’addanci a jihar Filato

0 217

Rundunar sojin hadin gwiwa ta Operation Safe Haven dake kokarin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar ta tabbatar da kama mutane 39 da ake zargi da aikata ta’addanci a jihar.

An gudanar da kamen ne a wurare daban daban tare da hadin gwiwar jami’an tsaron Operation Safe Haven da jami’an tsaro na Operation Hakorin Damisa da kuma sojojin runduna ta 3 cikin makon da ya gabata.

Kakakin rundunar Kaftin Oya James, shi ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Talata. Ya kara da cewa biyu daga cikin wadanda ake zargin suna jerin sunayen masu hannu a cikin yan fashi da makami a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: