Wata mata ta kashe dan kishiyarta dan kimanin kwanaki hudu a duniya

0 263

Wata mata mai suna Furera Abubakar mai shekaru 24 a duniya ta kashe dan kishiyarta dan kimanin kwanaki hudu a duniya a kauyen Bantu dake cikin karamar hukumar Ningi ta jihar Bauchi.

Kakakin rundunar ‘Yan sanda a jihar SP Ahmed Wakil shi ne ya tabbatar da kama wacce ake zargin cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata.

Wakil, yayi bayanin cewa an kai rahoton faruwar lamarin zuwa ofishin yan sanda dake Ningi a ranar 19 ga watan Augusta 2023, kwanaki bayan haihuwar jaririn.

SP Wakili, ya kara da cewa yanzu haka ana cigaba da gudanar da bincike inda daga bisani za a gurfanar da wacce ake zargin a gaban kotu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: