Magidanta 400,000 za su amfana da tallafin rage radadi n cire tallafin man fetur a jihar Borno

0 255

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, yace gwamnatinsa zata kara yawan adadin magidanta da za su amfana da tallafin rage radadi daga dubu dari uku zuwa dubu dari hudu.

Zulum, ya bayyana hakan ne jiya a Maiduguri inda yace hakan ya biyo bayan samun tallafin kudi naira bilyan biyar daga gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu domin rage radadin cire tallafin man fetur ga al’ummar jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa kowanne magidanci dake dauke da iyalai shida adadin ya karu zuwa dubu dari hudu wanda mutane milyan biyu da dubu dari hudu za su ci gajiyarsa.

Gwamna Zulum ya kara da cewa wannan rabon kayan talllafi hadin gwiwa ne tsakanin gwamnatin tarayya da jiha da kuma kananan hukumomi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: