‘Yan adawa na zargin magudi a zaben shugaban kasa dana yan majalisa a kasar Zambabwe

0 256

Yan kasar Zambabwe na kada kuri’a a zaben shugaban kasa dana yan majalisa.

Zaben dai na cike da rudani bayan yan adawa na zargin magudi yayin da a bangare guda jama’ar kasar ke fargabar shiga rikicin tattalin arziki.

Shugaba Emmerson Mnangagwa mai shekaru 80 a duniya wanda ya ke rike da kasar bayan dawo da mulkin farar hula lokacin marigayi Robert Mugabe 2017 na sake neman yin tazarce.

Za a rufe ofishoshin zabe daga karfe bakwai na dare agogon GMT, yayin da za a bayyana sakamakon karshe na zaben nan da kwanaki biyar masu zuwa

Leave a Reply

%d bloggers like this: