An kama mutane 4 da take zargi da fataucin mutane tare da ceto mutane 19 da ake shirin safararsu a jihar Jigawa

0 296

Darakta Janar na hukumar dakile safarar mutane, Bashir Garba Muhammad, a yau yace hukumar ta kama mutane 4 da take zargi da fataucin mutane tare da ceto mutane 19 da ake shirin safararsu.

Garba Muhammad, wanda ya samu wakilci kwamandan hukumar na shiyyar Kano, Abdullahi Babale, ya sanar da haka lokacin da yake yiwa manema labarai jawabi a Kano.

A cewarsa, mutane 4 da ake zargi, maza ne, yayin da wadanda aka ceto mata ne wadanda shekarunsu ya kama daga 14 zuwa 29.

Ya kara da cewa hukumar ta karbi rahoton leken asiri cewa wadanda ake zargin sun boye wadanda za ayi safararsu a nan jihar Jigawa, kafin daga bisani a tafi dasu a rukuni-rukuni zuwa jamhuriyar Nijar.

Garba Muhammad ya kuma ce hukumar ta ceto wasu yara biyar da ake sakawa aikin wahala sosai tare da damke wasu mutane biyu da ake zargi.

A cewarsa, yaran mata ne, da shekarunsu ya kama daga 10 zuwa 11.

Leave a Reply

%d bloggers like this: