An kashe mutane da dama a harin da ‘yan bindiga suka kai jihar Yobe

0 83

Wasu da ake tsammanin mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari ƙauyen Mafa a ƙaramar Hukumar Tarmuwa da ke jihar Yobe a arewacin Najeriya, tare da kashe mutanen da har yanzu ba a san yawansu ba.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya rawaito cewa, maharan sun yi sace-sace da yawa tare da banka wa shaguna da gidaje wuta a ƙauyen.

Kakakin ‘yan sanda na jihar Yobe Dungus Abdulkarim ne ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Litinin.

“Har yanzu muna aiki ne domin tabbatar da adadin mutanen da suka rasu dalilin wannan hari, wanda aka kai a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 4 na yamma.

“Wasu mutane da ake kira Babagana Goni da Bako Ibrahim ne suka shigar da ƙorafi kan harin a ofishin ‘yan sanda da ke Tarmuwa, kuma dukansu mazauna yankin Mafa ne.

“Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne ɗauke da makamai sun kai hari yankin Mafa a kan babura su sama da 50 kuma sun cinna wa shaguna da gidaje da yawa wuta.

Maharan sun kashe mutane da dama, amma har yanzu ba mu ƙididdige adadin waɗanda harin ya shafa ba,” in ji kakakin ‘yan sandan.

Ya ce bayan sun gama kai harin sun bar wasu makamai da rubutun larabci a jikinsu.

A ranar Juma’a NAN ya rawaito cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai hari wata makaranta da ke kusa da garin Geidam tare da kashe ɗalibai uku da jikkata ɗaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: