An ware Naira biliyan 8.3 domin gyara da sake gina tituna a Jigawa – Engr. Abbas Lalai

0 175

Gwamnatin jihar Jigawa ta ware naira biliyan 8.3 domin gyara da sake gina tituna, gadoji, da magudanan ruwa da ambaliyar ruwa ta lalata.

Gwamnatin jihar ta bude kwangilar gyara da sake gina ababen more rayuwa da suka lalace da suka hada da tituna da gadoji da ambaliayar ruwa ya shafa.

Hanyoyin da abin ya shafa sun hada da, Madobi-Katanga-Dangoli, Koriya-Gwiwa, Zakirai-Ringim, Gujungu-Hadejiya, da Gwaram-Basirika.

A cewar manajan daraktan hukumar kula da tituna ta jihar Jigawa (JIRMA), Engr. Abbas Muhammad Lalai, gyaran na da nufin dawo da harkokin zamantakewa da tattalin arziki a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: