An samu rahoton cin zarafin mata 24, 955 a jihar Legas
Hukumar da ke yaki da cin zarafin mata ta jihar Legas (DSVA) ta ce ta samu rahoton cin zarafin mata 24, 955 a jihar tsakanin shekarar 2019 zuwa yau.
Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar, Lawal Pedro, SAN da Babban Sakataren Hukumar DSVA ta Jihar Legas, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai na tunawa da watan wayar da kan jama’a da cin zarafin mata da ake yi a cikin gida, da kuma bayar da lambar yabo, wanda aka gudanar a Alausa. Ikeja.
A cewarsu, sun kuduri aniyar shawo kan matsalar cin zarafin mata da ke kara ta’azzara, inda suka kara da cewa gwamnatin jihar ta bayyana shirin fara gangamin yakin neman zabe a dukkanin kananan hukumomin jihar.
Pedro, wanda mukaddashin lauya Janar kuma babban sakatare, Hameed Oyenuga, ya wakilta, ya yi tir da yadda ake samun karuwar cin zzrzfin mata a jihar.