An kara wa Kwamishinonin ‘yan sanda 8 girma zuwa mukamin Mataimakin Sufeto-Janar na ‘yan sanda

0 115

Hukumar kula da ‘yan sanda ta kasa, PSC, ta amince da karin girma ga kwamishinonin ‘yan sanda takwas zuwa mukamin mataimakin sufeto-Janar na ‘yan sanda da wasu manyan jami’ai 676 zuwa sabbin mukamai. 

Ikechukwu Ani, shugaban yada labarai da hulda da jama’a na PSC ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa jiya a Abuja.

Mista Ani ya ce an kara wa mataimakan kwamishinonin ‘yan sanda 15 karin girma zuwa mukamin kwamishina CP yayin da manyan Sufeto Janar na ‘yan sanda 52 suka samu karin girma zuwa mataimakin kwamishinonin ‘yan sanda, ACP.

A cewarsa, Sufeto Janar na ‘yan sanda 525 sun samu karin girma zuwa babban Sufeto na ‘yan sanda CSP yayin da mataimakan Sufiritandan DSP 84 aka karawa SP.

Mista Ani ya ce shugaban ya umurci sabbin jami’anda aka kara wa karin girma da su kasance masu kishin cikinsu, su kuma shiryar fuskantar kalubalen aikin ‘yan sanda na karni na 21.

Leave a Reply

%d bloggers like this: