An samu karuwar masu dauke da cutar Mpox zuwa 48 a Najeriya – NCDC

0 97

Cibiyar dakile yaduwar Cututtuka ta kasa (NCDC) ta ce an samu karuwar masu dauke da cutar Mpox zuwa 48 a fadin kananan hukumomi 35 a cikin jihohi 19 da babban birnin tarayya (FCT).

Hakan na kunshe ne a cikin rahoton da cibiyar ta bayyana a  shafinta na sada zumunta a jiya. 

NCDC ta ce ba a sami rahoton mutuwa daga cutar ba ya zuwa yanzu a cikin 2024.

An samu rahoton bullar cutar a jihohin Legas, Rivers, Bayelsa, Abia, Delta, Imo, Edo, FCT, Anambra da Cross River.

Sauran jihohin da suka kamu da cutar sun hada da Plateau, Akwa Ibom, Nasarawa, Oyo, Kaduna, Ebonyi, Benue, Enugu, Osun, Kebbi, da Zamfara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: