An lalata maboyar ‘yan ta’adda, an kuma kashe da dama cikinsu a jihohin Zamfara da Sakkwato
Rundunar sojin hadin gwiwa ta Operation Hadarin daji dake aiki a yankin Arewa maso Yamma, sun lalata maboyar ‘yan ta’adda, tare da kashe da dama daga cikinsu da kuma kwato makamai da alburusai a jihohin Zamfara da Sakkwato.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Captain Ibrahim Yahaya, ya rabawa manema labarai jiya.
Yahaya ya ce dakarun sun zafafa kai hare-hare kan ‘yan ta’addan domin tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyi.
Ya ce, dakarun Operation Hadarin daji ne suka gudanar da aikin a kauyukan Dada, da Rukudawa da Dumburum a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara. Yahaya ya bayyana cewa, a wani samame da sojojin suka yi, sun kwato bindigogi biyu, da babura biyu, da kakin soja daban-daban, da kuma na’urorin sadarwa da alburusai.