Hukumar kidaya ta kasa, NPC ta kaddamar da binciken lafiyar al’umma a Najeriya

0 188

Hukumar kidaya ta kasa ta kaddamar da binciken lafiyar al’umma a Najeriya na shekarar 2023-2024. Haka nan kuma hukumar za ta fara aikin sake ginin ofishin hukumar na jihar Akwa Ibom a hukumance domin gudanar da aikin kidaya.

Shugaban hukumar kidaya ta kasa, Nasir Isa Kwarra, shine ya bayyana hakan lokacin da yake bikin kaddamar da shirin.

Ya kara da cewa hukumar zata yi abin da ya kamata wajen samar da abubuwan da suka dace domin samar da kyakkyawan yanayin aiki ga ma’aikatanta.

Shugaban hukumar kidayar wanda kwamishinan tarayya na jihar Akwa Ibom, Benedict Ukpong ya wakilta, ya bayyana cewa ginin da aka yiwa kwaskwarima domin dacewa da zamani wani bangare ne na shirye-shiryen kidayar jama’a da gidaje na kasa da za a yi nan gaba. Ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu kan tallafin kudi wanda ya sanya aka yi bikin kaddamarwar, ya kuma yabawa ma’aikatan hukumar NPC bisa jajircewa da kuma kokarin da suka yi na tsawon shekaru.

Leave a Reply

%d bloggers like this: