Kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattawa da na wakilai kan harkokin ‘yan sanda sun bukaci ministan harkokin ‘yan sanda da sufeto janar na ‘yan sanda su dauki matakan da suka dace domin inganta harkokin tsaro a kasar nan.
Kwamitin karkashin jagorancin Sanata Abdulhamid Mallam Madori da Makki Abubakar Yalleman, ya bayyana haka ne a lokacin da ministan da babban sufeton ‘yan sanda na kasa suka bayyana a gaban kwamitin a Abuja domin kare kasafin kudin 2024.
Kwamitin ya ce tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar kasa ya kasance babban nauyi ne da ya rataya a wuyan kowace gwamnati, don haka akwai bukatar ‘yan sandan Najeriya su ninka kokarinsu.
Makki ya bayyana cewa majalisar dokokin kasa za ta yi abin da ya kamata don ganin an yi abubuwan da suka dace domin inganta ayyukan ‘yan sandan Najeriya. Ministan harkokin ‘yan sanda, Ibrahim Gaidam, ya ce ma’aikatar tana aiki da ‘yan sanda da sauran cibiyoyi domin ganin sun gudanar da aikinsu na tabbatar da tsaron cikin gida.