Gwamnatin jihar Kano ta amince ta biya diyyar kudi naira biliyan 3

0 121

Gwamnatin jihar Kano ta amince ta biya diyyar kudi naira biliyan 3 ga kungiyar masu rike da shagunan Masallacin Idi saboda rusa musu kadarorin da aka yi ba bisa ka’ida ba.

An cimma wannan matsaya ne ta wata bukata ta neman sulhu a ranar 12 ga watan Disamba da kuma ranar 13 ga watan Disamba da lauyoyin bangarorin suka shigar a gaban mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja. Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, biyo bayan rusa shagunan da aka yi bisa umarnin Gwamna Abba Yusuf, masu neman biyan diyya 56 a madadin kungiyar, sun shigar da kara a sashin kotun dake jihar Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: