Gwamna Namadi ya yabawa gwamnatin tarayya bisa gudanar da ayyukan raya kasa a jihar Jigawa

0 214

Gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar Namadi ya yabawa gwamnatin tarayya bisa gudanar da ayyukan raya kasa daban-daban a fadin jihar.

Gwamnan ya yi wannan yabon ne a lokacin da ya jagoranci mika fitilun kan titin Kiyawa zuwa Kwanar Huguma a hukumance daga ma’aikatar ayyuka ta tarayya zuwa gwamnatin jihar Jigawa.

Bikin mika aikin ya yi nuni da irin kokarin hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin jihohi da na tarayya domin inganta ababen more rayuwa da inganta rayuwar al’ummar jihar.

Da yake bayyana godiyarsa, Gwamna Mallam Umar Namadi ya godewa ma’aikatar ayyuka ta tarayya da gwamnatin tarayya bisa muhimmiyar rawar da suke takawa wajen aiwatar da wannan aiki. Ya kuma jaddada kudirin gwamnatinsa na yin aiki tare da gwamnatin tarayya domin kawo sauyi mai kyau ga al’ummar jihar Jigawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: