Gwamnonin Arewa 19 zasu matsa lamba ga hukumomi don yi wa mutanen Tudun-Biri adalci

0 226

Gwamnonin Arewa 19 sun amince su yi matsin lamba ga hukumomi don ganin an yi wa mutanen Tudun-Biri adalci, bayan harin bam da sojojin kasar suka kai musu bisa kuskure a jihar Kaduna.

Kazalika gwamnoni sun yi kira da a gudanar da bincike kan lamarin, suna masu fatan wannan tsautsayin ba zai sake faruwa ba a Najeriya.

Shugaban Kungiyar Gwamnoni kuma Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya bayyana haka a wurin kaddamar da taronsu a wannan Juma’ar a jihar Kaduna.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin ya bukaci gwamnonin da su yi shiru na tsawon minti guda domin karrama mutanen da suka rasa rayukansu a sanadiyar harin na Tudun-Biri, yana mai cewa, kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu, nauyi da ya rataya a wuyen gwamnati.

Ya kuma jinjina wa gwamnatin tarayya kan yadda ta yi gaggawar mayar da martani jim kadan da faruwar lamarin.

A bangare guda, gwamnonin sun bai wa mutanen na Tudun-Biri tallafin naira miliyan 180. Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin sake gina garin karkashin wani shirinta na Fulako kamar yadda mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana a lokacin da ya ziyarci mutanen da harin ya rutsa da su a asibiti a jihar Kaduna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: