Ƙungiyar ‘yan kwadago NLC ta yi Allah wadai da shawarar ƙara farashin man fetur zuwa ₦‎750

0 182

Ƙungiyar ‘yan kwadago ta kasa NLC ya Allah wadai da shawarar da Bankin Duniya ya bai wa gwamnatin tarayya na ƙara farashin man fetur zuwa naira 750 duk lita ɗaya.

Shugaban NLC Joe Ajaero ne ya bayyana haka a jiya Juma’a a Abuja cikin wata sanarwa da suka fitar.

Mista Alex Sienaert wanda shi ke jagorantar masana tattalin arzikin Bankin Duniya a Najeriya, shine ya bayar da wannan shawara yayin gabatar da wata maƙala ta halin da ake ciki kan ci gaban Najeriya na Disamba 2023. Masana tattalin arzikin sun fahimci cewa har yanzu gwamnatin na ci gaba da biyan tallafin man fetur, hakan ya sa suka bayar da shawarar a ƙara farashin zuwa naira 750.

Leave a Reply

%d bloggers like this: