Mele Kyari ya kalubalanci sammacin kama shi kan binciken Naira tiriliyan 210

0 126

Tsohon Shugaban Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), Mele Kyari, ya bayyana matukar mamakinsa kan sammacin kama shi da Kwamitin Kula da Asusun Jama’a na Majalisar Dattawa ya fitar, yana mai cewa tun da farko ya sanar da kwamitin cewa yana jinya a kasashen waje.

A wata wasika da ya aikewa kwamitin mai dauke da kwanan watan 10 ga Yuni, 2026, Kyari ya ce ya riga ya rubuta wa kwamitin tun ranar 8 ga watan Mayu, inda ya sanar da su cewa yana wajen Najeriya domin samun kulawar lafiya, kuma hakan ne ya hana shi halartar zaman binciken.

Ya jaddada cewa rashin halartarsa ba yunkurin kaucewa binciken da ake yi ba ne, illa dai sakamakon halin da yake ciki na rashin lafiya.

Kyari ya bayyana cewa yana da cikakken shirin ba da hadin kai ga kwamitin, tare da amsa duk wasu tambayoyi da za a yi masa da zarar ya dawo gida Najeriya.

Tsohon shugaban na NNPCL ya kuma ce ya bayar da shawarar a aiko masa da tambayoyin kwamitin ta hannun lauyoyinsa domin ya bayar da bayanai ba tare da jinkirta aikin binciken ba.

Ya kara da cewa duk harkokin kudade da mu’amalolin da aka gudanar a lokacin mulkinsa an adana su yadda ya kamata, kuma ana iya tantance su a cikin bayanan kamfanin.

Tun da farko dai Kwamitin Kula da Asusun Jama’a na Majalisar Dattawa ya bayar da umarnin kamo Mele Kyari bayan ya kasa bayyana a gabansa domin amsa tambayoyi kan wasu bayanan kudade na NNPCL daga shekarar 2017 zuwa 2023.

Kwamitin na binciken wasu tambayoyin tantance kudade guda 19 da Ofishin Babban Mai Binciken Kudi na Tarayya ya gabatar, ciki har da zargin rashin cikakken bayani kan sama da Naira tiriliyan 210 na kudaden kamfanin.

An amince da fitar da sammacin ne bayan sanatoci sun nuna rashin gamsuwa da rashin halartar Kyari, inda wasu suka dage cewa dole ne ya bayyana domin bayar da cikakken bayani kan zarge-zargen da ake bincike.

Leave a Reply