Sanata Sabo Nakudu Ya Yabawa INEC Kan Maido Da Mazabar Aujara, Ya Ce Nasara Ce Ga Dimokiraɗiyya

0 140

Sanata Sabo Mohammed Nakudu, CON, ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Jihar Jigawa, ya taya al’ummar Aujara da ke Ƙaramar Hukumar Jahun murnar maido da Mazabar Jiha ta Aujara, bayan amincewar da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayar.

A cikin saƙon taya murnarsa, Sanatan ya bayyana matakin a matsayin wani babban ci gaba da ya dawo da haƙƙin dimokiraɗiyya da aka daɗe ana jira, tare da ƙarfafa adalci, haɗin kai da kuma wakilci mai inganci a siyasar jihar.

Ya ce maido da mazabar ba wai nasara ce ga al’ummar Aujara kaɗai ba, har ila yau wata gagarumar nasara ce ga tsarin dimokiraɗiyya da tabbatar da adalci a harkokin mulki.

Sanata Nakudu ya bayyana cewa al’ummar Aujara sun nuna haƙuri da jajircewa tsawon shekaru wajen neman dawo da wakilcinsu, yana mai cewa wannan nasara ta sake ba su damar samun cikakken wakilci a Majalisar Dokokin Jihar Jigawa.

Ya kuma yi kira ga al’ummar sabuwar mazabar da su ci gaba da zama cikin haɗin kai da zaman lafiya, yayin da jam’iyyun siyasa ke shirin gudanar da zaɓukan fidda gwani kafin babban zaɓen shekarar 2027.

Sanatan ya ƙarfafa mazauna yankin da su yi amfani da wannan dama wajen ƙara shiga harkokin jama’a da kuma tallafa wa zaɓen shugabanni nagari.

Haka kuma, ya yabawa INEC, ɓangaren shari’a, shugabannin siyasa da na al’umma, tare da dukkan waɗanda suka taka rawa wajen tabbatar da wannan nasara, yana mai cewa ƙoƙarinsu ya ƙara ƙarfafa amincewar jama’a ga cibiyoyin dimokiraɗiyya.

A madadin iyalansa, magoya bayansa da jam’iyyar ADC, Sanata Sabo Mohammed Nakudu ya sake taya al’ummar Aujara murna, tare da fatan cewa wannan sabon babi zai samar da ƙarin fata, ci gaba mai ɗorewa da kuma faɗaɗa shigar al’umma cikin harkokin mulki a nan gaba.

Leave a Reply