An Maka Tinubu A Kotu Ana Neman Hana Shi Takara A Zaɓen 2027

0 129

An maka Tinubu a kotu ana neman hana shi takara a Zaɓen 2027

An shigar da wata ƙara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Kano wadda ke neman a hana Shugaba Bola Tinubu tsayawa takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2027.

Ƙungiyar Centre for Reform and Public Advocacy (CFRPA) da ke fafutikar kare haƙƙin ɗan Adam ce ta shigar da ƙarar, inda ta zargi Tinubu da gabatar da takardun karatu da ta ce ba sahihai ba ne ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) a lokacin Zaɓen 2023.

A ƙunshin ƙarar mai lamba FHC/K/CS/312/2026, an sanya Tinubu da INEC da kuma Jami’ar Chicago da ke Amurka a matsayin waɗanda ake tuhuma.

Ƙungiyar mai zaman kanta wadda ke fafutukar tabbatar da dimokuraɗiya da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa, ta buƙaci kotun da ta umarci INEC ta hana Tinubu tsayawa takara a Zaɓen 2027, sannan ta ba da umarnin gabatar mata da takardun karatunsa.

Har yanzu kotun ba ta fara sauraron shari’ar ba, kuma ba ta yanke hukunci kan zarge-zargen da aka gabatar ba.

Ana iya tuna cewa a bayan nan ne CRFPA ta aike wa INEC wasiƙa tana neman ta fito fili ta bayyana matsayarta kan zargin takardun bogi na shaidar karatu na Shugaba Tinubu da ke da alaka da Jami’ar Chicago da ke Amurka.

Leave a Reply