An saki tsohon Shugaba Gabon, Ali Bongo tare da matarsa Sylvia da ɗansa Noureddin bayan kwashe kusan shekara biyu a tsare inda a halin yanzu sun bar ƙasar zuwa Angola
Iyalan dai sun fuskanci tuhuma kan cin hanci da rashawa tun bayan kifar da gwamnatin Bongo a juyin mulki na shekarar 2023.
Fadar shugaban Angola ta tabbatar da isowarsu birnin Luanda, gurin suka koma bayan wata ganawa tsakanin shugaban Angola João Lourenço da sabon shugaban Gabon, Brice Oligui Nguema.
Har yanzu ba a bayyana ko shari’ar da ake yi wa Sylvia da ɗanta za ta ci gaba ba.
Ali Bongo ya jagoranci Gabon na tsawon shekaru 14 bayan mahaifinsa, Omar Bongo, wanda ya mulki ƙasar sama da shekaru 40.
Duk da arzikin man fetur a ƙasar, kashi ɗaya bisa uku na al’ummar Gabon na rayuwa cikin talauci, lamarin da ya janyo suka kan dangin Bongo da zargin amfani da dukiyar ƙasa don amfanin kansu—zarge-zargen da suka musanta.