An samar da jami’an tsaro domin kawar da ‘yan ta’adda a Najeriya – Janar Lagbaja

0 118

Babban hafsan sojojin Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa an samar da jami’an tsaro domin kawar da ‘yan ta’adda, ‘yan fashi da sauran masu aikata laifuka.

Shugaban sojojin ya kara da cewa ya kuduri aniyar samar da zaman lafiya mai dorewa a kasar.

Najeriya dai na fama da kalubalen tsaro da suka hada da ta’addanci, da fashi da makami, da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

A sakonsa na bikin Esta a jiya Lahadi, Hafsan sojojin ya bayyana cewa rundunar ta samu nasarori da dama a ayyukan da take ci gaba da yi na yaki da ta’addanci da ‘yan fashi a kasar nan.

Lagbaja ya bayyana cewa ya bayar da horo da kayan aikin da ake bukata ga jami’an sa domin shawo kan matsalar rashin tsaro da ke addabar kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: