Karancin kudi ne ya janyo tsaikon aikin layin dogo na Fatakwal zuwa Aba

0 92

Gwamnatin tarayya ta ce karancin kudi ne ya janyo tsaikon aikin layin dogo na Fatakwal zuwa Aba da aka samar da nufin bunkasa tattalin arzikin kasar nan.

Kwanan nan ne Ministan Sufuri, Saidu Alkali, ya bayyana haka ga manema labarai a Jihar Ribas, a lokacin da yake duba aikin.

Alkali ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na iya bakin kokarinta wajen samar da kudaden ci gaba da aikin.

A cewarsa, gwamnatin da ta shude ce ta bayar da wannan aikin wanda yace gwamnati mai ci ta na kokari wajen samar da dukkan tsare-tsare na kudi kafin fara aikin. Ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a fara aikin nan take da zarar an shawo kan matsalar kudi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: