Kalubalen da Najeriya ke fuskanta sun samo asali ne tun lokacin Turawan mulkin mallaka – Obasanjo
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce wasu daga cikin ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta a yanzu sun samo asali ne tun lokacin Turawan mulkin mallaka.
Obasanjo ya bayyana haka ne a ranar Asabar a Enugu lokacin da yake gabatar da wata maƙala ta littafi wanda Chris Okoye ya rubuta.
Cikin wata sanarwa da Kehinde Akinyemi, mai taimakawa Obasanjo kan yada labarai na musamman ya fitar ta ce tsohon shugaban kasar ya ce akwai alaƙa ta kai tsaye tsakanin tattalin arziki da sauya tsarin siyasa. Ya ce tarihin yadda aka samar da kundin mulkin Najeriya da kuma titin da aka dora siyasar ƙasar na nuna akwai wani giɓi da aka bari, wanda yake buƙatar a cike shi domin sake faɗaɗa ka’idojin dimokraɗiyyar Najeriya.