Jam’iyyar PDP reshen jihar Jigawa ta yi watsi da kiran da majalisar ta bayarda shawarwari ga dukan jam’iyyu reshen jihar nan na a kara wa’adin shekara guda domin gudanar da zaben kananan hukumomi.
An zabi shugabannin kananan hukumomi 27 na yanzu da kansiloli 287 a watan Maris na 2021 na tsawon shekaru uku.
A wani taro da aka yi a Dutse, IPAC, ta ce karin wa’adin zai ba da damar shirya yadda ya kamata a gudanar da zaben kananan hukumomin.
Da yake zantawa da manema labarai, shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Dutse, Alhaji Sa’adu Barwa Dutse, ya ce wasu tsirarun mutane a IPAC ne kawai suke kokarin tilasta wa masu rinjaye ra’ayin. Barwa ya zargi shugabancin IPAC dayin aiki da jam’iyyar APC mai mulki domin yin tilasta bin ra’ayin dage zaben.