An samu gawarwakin mutum 4 yan gida daya a wata gonar kiwon kaji a Abuja

0 125

An samu gawarwakin mutane hudu ‘yan gida daya a wata gonar kiwon kaji a karamar hukumar Abaji da ke babban birnin tarayya Abuja.

An rawaito cewa an samu gawar wani mai gadin gidan kajin mai suna Dominic Peter Adegeze, da ta ‘ya’yansa mata, Victoria da Judith, da ta dansa mai suna Peter dan wata daya da haihuwa, sannan an kai matarsa mai suna Laraba zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja a sume.

Wani ma’aikacin gidan kajin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce lamarin ya faru ne a jiya da safe, inda ya bayyana cewa wani ma’aikaci ne da ya je bawa shanu abinci a gidan kajin ya iske babbar kofar gidan a kulle da makulli, sai ya tsallaka katanga ya iske mai gadin da iyalinsa kumfa na fita daga bakunansu.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, DSP Adeh Josephine, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ‘yan sanda na gudanar da bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: