Mutum daya cikin goma a Najeriya ke farin ciki da mulkin Buhari – Binciken API

0 109

Wani sabon bincike da cibiyar API ta gudanar ya gano cewa mutum daya ne kawai cikin mutane goma a cikin ’yan Najeriya ke farin ciki da yadda al’amura ke tafiya a Najeriya a karkashin mulkin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Sakamakon binciken ya nuna cewa ya zuwa watan Janairu, kusan kashi 78 cikin 100 na ‘yan kasarnan ba sa jin dadin halin da kasar ke ciki; kusan rabin rabin adadin sunce suna bakin ciki matuka game da halin da kasarnan ke ciki.

Sauran kashi 14 cikin 100 na ‘yan kasarnan sun ce ba ruwansu da halin da kasar ke ciki.

API, cibiyar bincike mai zaman kanta, ta ce an gudanar da binciken ne don yin hasashe kan halayen ‘yan kasa dangane da batutuwan da suka shafi al’amuran zamantakewa, tattalin arziki, siyasa, mulki da kuma rayuwar jama’a.

Rahoton na API ya kuma ce kashi 34 cikin 100 na ‘yan Najeriya sun bayyana kasa biyan bukatunsu na yau da kullum a wani bangare na kalubalen da suke fuskanta. Hakan ba zai rasa nasaba da yanayin tattalin arzikin da ake ciki a kasarnan ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: