Babu wani uzuri na sauya gwamnati ta hanyar juyin mulki – ECOWAS

0 74

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS sun sake jaddada matsayarsu na cewa kwata-kwata babu wani uzuri na sauya gwamnati ta hanyar juyin mulki.

Ya bayyana hakan ne a jiya bayan halartar babban taron kungiyar ECOWAS da aka gudanar a Accra, babban birnin kasar Ghana, kuma tattaunawar da aka yi a taron ta shafi harkokin siyasa a kasashen Burkina Faso, Mali da Guinea.

Mataimakin shugaban kasar ya ce a ra’ayin kungiyar ECOWAS, hanya daya tilo ta sauya gwamnati a yankin da aka amince da ita, ita ce ta hanyar demokradiyya.

Farfesa Osinbajo wanda ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari a wajen taron, ya amsa tambayoyi daga manema labarai kan sakamakon taron.

A wata sanarwa da kakakinsa Laolu Akande ya fitar, ya ce mataimakin shugaban kasar ya dawo Abuja da yammacin jiya daga birnin Accra.

Leave a Reply

%d bloggers like this: