Gwamnatin jihar Zamfara ta bada gudunmawar Naira miliyan 7 ga iyalan yan sanda 7 da yan bindiga suka kashe

0 101

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bada gudunmawar Naira MIliyan 7 ga Iyalan Yan sanda 7 da yan bindiga suka kashe a Jihar.

Gidan Talabijin na Channels Tv, ya rawaito cewa a ranar 8 ga watan Nuwambar 2021 ne yan bindigar suka yiwa yan Sandan Kwantan Bauna tare da halaka su.

Kwamishinan yan sandan Jihar Zamfara CP Ayuba Elkana, shine ya mika Naira Miliyan 1 ga kowanne Iyalan yan sandan da suka mutu.

A cewarsa, gwamnatin Jihar Zamfara karkashin Jagorancin Gwamna Bello Matawalle ta mika kudaden ne ga Iyalan yan sandan da suka mutu a bakin aiki domin tallafawa rayuwar su.

Kwamishinan, ya ce Jami’an sun mutu ne a lokacin da suke bakin aiki domin kare kasar su da Al’ummar cikin ta, a kokarin da suke yi na dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso yamma.

Jami’an yan sandan da lamarin ya rutsa da su sun hada da Jonah Markus, Solomon Abiri, Stephen Ishaya, Nura Ibrahim, Abdul Garba, Musa Lawal and Zubairu Sadiq.

Leave a Reply

%d bloggers like this: