Gwamnati Tarayya ta amince da bada kudi fiye da naira miliyan dubu dari domin gudanar da aikin hanyar Kano zuwa Kazaure

0 135

Gwamnatin tarayya ta amince da bada kudi fiye da naira miliyan dubu dari da goma sha biyar domin gudanar da aikin maida hanyar kano- Kazaure-zuwa Kongwalan data ratsa jihohin Kano da Jigawa da kuma Katsina zuwa tagwayen Titi.

Ministan ayyuka da gidaje na kasa, Babatunde Fashola ne ya sanar da haka bayan kammala taron majalisar zartarwa na mako-mako wanda shugaban kasa Muhammad Buhari ya joranta a Abuja.

Ya ce ana sa ran kammala aikin mai nisan kilomita dari da talatin da daya da digo hudu cikin shekaru biyu masu zuwa.

Shima takwaran sa na ma’aikatar sifuri, Rotimi Amechi ya ce ,majalisar ta amince da kudi dala miliyan dari da tamanin da uku da dubu dari bakwai domin ayyukan kwararrun da za su sa ido kan wasu ayyukan gina titin Jirgin kasa guda uku a kasar nan.

Ayyukan sune na Fatakwal zuwa Maiduguri da Kano zuwa Maradi da kuma na Abuja zuwa Warri.

Leave a Reply

%d bloggers like this: