Mutum 42 sun sake harbuwa da cutar zazzabin Lassa a jihohi 5 na Najeriya

0 32

Cibiyar Dakile yaduwar cututtuka ta Kasa wato NCDC ta ce sabbin mutane 42 ne suka harbu da zazzabin Lassa cikin Jihohi 5 na kasar nan.

Zazzabin Lassa wanda ake dauka ta hanyar yin mu’amala da wanda ya ke dauke da cutar, tana da alamomin zazzabi, gudawa da sauran su.

A rahotan da NCDC ta fitar ya yi nuni da cewa daga ranar 24 zuwa 30 ga watan Janeru kimanin mutan 15 ne suka harda da zazzabin a Jihar Ondo sai Bauchi mai mutane 14 da kuma Edo mai mutane 10.

Sauran Jihohin sune Enugu da Delta.

Kawo yanzu adadin mutanen da suka harda da cutar cikin shekarar 2022 sun kai 211.

Hukumar ta ce mutane 6 zazzabin Lassa ya kashe cikin shekarar 2022.

Leave a Reply

%d bloggers like this: