Gwamna Badaru Abubakar ya amince da nadin karin sakatarori na kananan hukumomi uku

0 95

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na Jihar Jigawa ya amince da nadin sakatarorin wasu kananan hukumomi uku.

Wadanda aka nada sun hadar da Hon Lawan Suleiman, a matsayin Sakataren karamar hukumar Babura da Hon Ya’u Hussaini Kachallari a matsayin Sakataren Karamar Hukumar Birniwa da kuma Hon Sabo Wada Ringim a matsayin Sakataren karamar hukumar Ringim.

A sanarwar da kwamishinan kananan Hukumomi Alhaji Kabiru Hassan Sugungum ya bayar tace nadin ya fara aiki nan take.

Daga nan sanarwar ta taya su murnar nadin da aka musu tare da yin kira dasu kasance masu kwazo wajen gudanar da aiyukansu

Leave a Reply

%d bloggers like this: