Gwamnatin tarayya ta bawa jami’ar Sule Lamido dake Kafin Hausa naira miliyan 193 a matsayin kudaden asusun bincike

0 112

Jami’ar Jiha ta Sule Lamido dake Kafin Hausa ta karbi kudi sama da naira miliyan dari da casa’in da uku a matsayin kudaden asusun bincike bukatun karatu na shekara ta 2019 daga ma’aikatar ilimi ta tarayya.

Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da ofishin jami’in hulda da jama’a na Jami’ar ya bayar.

Ya ce anyi amfani da kudaden ne wajen sayo kayayyakin dakin gwaje-gwajen kimiya da kammala cibiyar Fasahar ilimi ta Jami’ar da kuma baiwa malaman horo kan aiki da wasu daga cikin kayyakin gwaje-gwaje.

Jami’in hulda da Jama’ar ya kara cewa anyi amfani da wasu daga cikin kudaden wajen sayen kayayyakin gwaje-gwaje na Kimiyya.

Sanarwar ta kuma yabawa ma’aikatar ilimi ta tarayya bisa shiga tsakanin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: