Kimanin mutum 6 ciki harda Bulama yan bindiga suka kashe a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina

0 155

Kimanin mutane 6 ne ciki harda Bulaman Gari yan bindiga suka kashe a kyauyen Daddara na karamar hukumar Jibia ta Jihar Katsina.

Kakakin rundunar yan sandan Jihar SP Gambo Isah, shine ya tabbatar da hakan, inda ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na Dare.

SP Gambo Isah, ya ce daruruwan yan bindigar sun farmakin kyauyen ne akan Babura dauke da muggan Makamai, inda suka yi awun gaba da Bindigogi.

A cewarsa, yan bindigar sun yi kokarin sa ce mutane da dama a kyauyen sai dai Jami’an tsaro sun hada su.

Gambo Isah, ya ce yan bindigar sun kashe mutane 6 a kyauyen  tare da raunata mutane 5 wanda a yanzu haka suke samun kulawar likitoci.

Kazalika, ya ce an tura Jami’an tsaro zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: