An samu dan karamin rikici yayin wani taron raba kayan tallafi ga mata a Fatakwal, ta jihar Ribas, karkashin shirin ajandar sabunta fata, na uwargidar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu.
Wasu mata sun fice daga dakin taron bayan an bai wa uwargidar mai rikon mukamin gwamnan jihar, Theresa Ibas, damar yin jawabi, maimakon uwargidar gwamna da aka dakatar, Valerie Fubara.
To amma dai an cigaba da gudanar da taron cikin kwanciyar hankali inda aka raba kayan aiki ga mata 500 da aka zaba daga kananan hukumomi 23 na jihar.
Kayayyakin sun hada da firiji, injin markade, da janareto, wadanda aka ce za su taimaka wa mata su fara ko kuma fadada kasuwanci domin bunkasa tattalin arziki.