Gwamnatin tarayya ta bukaci sabon babban kwamandan Hukumar Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya, Sylvester Nwakuche, da ya jagoranci sauyi daga tsarin hukunta fursunoni zuwa tsarin gyara da ingantawa.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana haka a yayin bikin nadin da aka gudanar a Abuja, inda ya jaddada cewa shugabanci da hangen nesa su ne ginshikan nasara.
A nasa jawabin, CG Nwakuche ya bayyana wannan dama a matsayin kira zuwa ga ma’aikata, tare da gabatar da tsare-tsaren sauyi guda bakwai da suka hada da rage cunkoso, da kuma inganta lafiyar firsunoni.
Ya ce za su kara daukar ma’aikata, wadan da za suyi amfani da na’urori masu lura da yanayi domin tabbatar da tsaro da kyautata rayuwar fursunoni.