Hukumar Kwastam ta Najeriya ta musanta zargin da ake mata na yunƙurin dawo da harajin FOB

0 592

Hukumar hana fasakwauri ta Najeriya (kwastam)ta musanta zargin da ake mata na yunƙurin dawo da harajin FOB.

A Najeriya, hukumar kwastam ta musanta zancen da ake yi cewa, za ta dawo da nau’in harajin na kashi huɗu cikin ɗari da ake cirewa na shigar da kaya cikin ƙasar, wanda ake kira ”FOB”, wanda aka ɗage aiki da shi a ƴan watannin baya.

Hukumar ta ce, ko da za a ci gaba da aiki da wannan haraji, sai an zauna da dukkan masu ruwa da tsaki, a tattauna da su.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar AbdulLahi Aliyu Maiwada ne ya yi BBC wannan ƙarin bayani, inda ya ƙara da ba zai yiwu a dawo da karɓar harajin ba ta bayan fage ba tare da an zauna an daddale tare da fahimtar juna ba.

Leave a Reply