Tattalin arzikin Najeriya a yanzu ya fi muni fiye da lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Buhari

0 444

Tsohon mai bai wa Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima shawara kan harkokin siyasa, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya ce halin tattalin arzikin Najeriya a yanzu ya fi muni fiye da lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A cikin wata hira da ya yi da Channels TV a shirin *Politics Today*, Baba-Ahmed ya bayyana cewa tsarin cire tallafin man fetur da sauya tsarin musayar kudade sun kara jefa ‘yan Najeriya cikin tsananin yunwa da talauci, yana mai nuna cewa hauhawar farashi daga kashi 22.41% zuwa 34.6% cikin shekara guda na nuna tabarbarewar tattalin arziki.

Ya ce yawancin alkaluman da gwamnatin ke fitarwa na nuna cigaba be dace da hakikanin abinda ke faruwa a kasa ba, inda ya jaddada cewa jini na zuba fiye da yadda aka taba gani a baya.

Baba-Ahmed ya kuma ce shugaban kasa Tinubu ya kamata ya dakatar da kudurin sake tsayawa takara a zaben 2027, maimakon haka ya maida hankali kan gyaran kasa da kuma barin zaben da ke tafe na 2027 ga matasa masu hangen nesa da kwazo.

Leave a Reply