An samu musayar yawu tsakanin INEC da majalisar kasa dangane da aikawa da sakamakon zabe ta na’ura

0 71

An samu musayar yawu tsakanin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da majalisar kasa, dangane da aikawa da sakamakon zabe ta na’ura.

Bisa watsi da matsayar majalisar kasa na umartar hukumar zaben da ta samu sahalewar hukumar sadarwa ta kasa (NCC) dangane da aikawa da sakamakon zaben ta na’ura, hukumar INEC tace kundin tsarin mulki bai tilasta mata hakan ba.

Kafin a tafi hutun majalisa a watan Yuli, majalisar kasa a lokacin da take kada kuri’a dangane da gyaran dokar zabe, tayi fatali da sashen dake magana akan hukumar INEC ta aika da sakamakon zabe ta na’ura, inda majalisar tace kasarnan bata kai matsayin haka ba.

Dokar hukumar zabe da aka gyara, idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya mata hannu, ana sa ran zata karfafa ingancin zaben kasarnan.

A zaman ganawar jiya tare da ‘yan jaridu da kungiyoyin fararen hula, shugaban INEC, Mahmud Yakubu, ya nanata aniyar hukumar na cigaba da tabbatar da sahihancin zabe ta hanyar shigo da tsarin amfani da na’ura.

Leave a Reply

%d bloggers like this: