Hukumar tsaro ta kama wasu mutane 3 da take zargi da satar babur a jihar Jigawa

0 68

Hukumar tsaron fararen hula civil defense a jihar Jigawa ta kama wasu mutane uku da take zargi da satar babur da karbar kayan sata.

Kakakin hukumar na jiha, Adamu Shehu, ya gayawa kamfanin dillancin labarai na kasa yau a Dutse cewa an kama wadanda ake zargin a yankin karamar hukumar Kafin Hausa ta jihar.

Adamu Shehu yace jami’an hukumar sun kama mutane biyu daga cikin wadanda ake zargin, yan shekaru 19 da 20, kuma sun fito ne daga garuruwan Turakawa da Gafasan-Turawa.

Kakakin ya kara da cewa wadanda ake zargin sun kuma amince cewa wani mai suna Dauda Auwalu ne ya umarce su da su sace babur din kuma zai biya su naira dubu 55 saboda hakan.

Yace daga baya jami’an hukumar sun kama Dauda Auwalu tare da babur da ake zargin sato shi aka yi.

Yace nan bada jimawa ba, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: