‘Yan fashin daji sun mamaye karamar hukumar Dange Shuni a jihar Sokoto inda suka sace akalla mutane 20

0 81

‘Yan fashin dajin da ake zargin suna gujewa hare-haren sojin saman Najeriya a yankin Bakura da Talatan Mafara na jihar Zamfara, a jiya sun mamaye karamar hukumar Dange Shuni a jihar Sokoto, inda suka sace akalla mutane 20.

Kwamishinan harkokin tsaro na jihar Sokoto, Garba Moyi, ya tabbatar da aukuwar lamarin amma yace gwamnatin jihar tana bisa turbar dakile shi.

Ana cigaba da fatattakar ‘yan fashin daji a dazukan jihar Zamfara.

Aikin sojojin ya samu tallafin toshe kafofin sadarwar wayar salula da dakatar da kasuwannin shanu da kuma haramta sayar da man fetur a jarkoki.

Jihoshi irinsu Sokoto da Katsina da Neja suma sun dauki irin wannan matakan.

Sai dai, mazauna karamar hukumar Dange Shuni a jihar Sokoto sun shaidawa BBC Hausa cewa kauyukan karamar hukumar na fuskantar barazanar kwararowar ‘yan fashin daji a ‘yan kwanakinnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: