An samu mutuwar mutane 83 yayin da 836 aka tabbatar sun kamu da cutar sarkewar numfashi

0 247

Hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko ta kasa ta ce an samu mutuwar mutane 83 yayin da 836 aka tabbatar sun kamu da cutar sarkewar numfashi farkon shekarar nan.

Babban Daraktan hukumar Faisal Shuaib ne ya bayyana haka a ranar Litinin a Abuja yayin da yake ganawa da manema labarai game da bullar cutar.

Ya ce, daga watan Mayun 2022 zuwa Yuli 2023, an yi kiyasin mutane 2,455 da ake zargin sun kamu da cutar a jihohi 26 zuwa ranar 27 ga Yuli, 2023, an tabbatar da 836 da suka kamu da cutar a  kananan hukumomi 33 a fadin jihohi takwas: Cross River, Kano, Katsina, Kaduna, Lagos, Osun, Yobe, da FCT.

Ya zuwa yanzu, an bayar da rahoton mutuwar mutane 83 daga wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar.

Shuaib ya ce, duk da kokarin da Gwamnatin Tarayya ta yi na samar da lafiya da alluran rigakafin cutar amai da gudawa, akwai adadi mai yawa na kananan yara da ba a yi musu allurar riga-kafi ba ko kuma a yi musu wani bangare na allurar, wanda hakan ke kawo cikas ga burin kasar na samun rigakafin cutar.

Shugaban hukumar UNICEF a Najeriya Eduardo Celades, ya ce kashi 70 cikin 100 na yaran da ke fama cutar a Najeriya sun haura shekaru biyu kuma kashi 80 cikin 100 ba a yi musu allurar rigakafi ba ko kuma ba su kammala allurar ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: