Ma’aikatar harkokin kasasen wajen Faransa tace nan gaba kadan zata fara kwashe yan kasar ta daga jamhuriyar Nijar biyo bayan juyin mulki da sojoji sukayi a kasar.
Ofishin jakadancin Faransa a Yamai yace sakamakon rashin tsaro a kasar, hakan yasa ta shirya debe yan kasar ta daga Nijar din.
A makon da ya gabata ne sojoji suka yiwa shugaban kasar Bazoum juyin mulki.
Nijar ce kasa ta uku da aka yiwa juyin mulki a yankin Sahara,baya ga Burkina Faso da Mali a kasa da shekaru uku.
Lamarin ya sa kasashen ke kin jinin Faransa,tare da kulla alakar kut-da kut da kasar Rasha.