Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jibiya/Kaita a Jihar Katsina, Hon. Sada Soli Jibiya, ya bayyana cewa an san ‘yan bindigar da suka kai hari masallaci suka kashe mutane fiye da 30 a lokacin sallar Asuba.
Da yake zantawa da gidan talabijin na Channels TV a shirin Politics Today, Soli ya ce ‘yan bindigar na rike da wasu yankuna ne a jihar, inda babu wani hukuma ko jami’in tsaro da ke da iko a wuraren.
“Ba su zo daga wata kasa ko wata duniya ba. Mutane ne da ke zaune a tsakaninmu. Hatta jami’an tsaro sun san su,” inji dan majalisar.
A cewar sa, wannan hari da ya afku a karamar hukumar Malumfashi, na da nasaba da yawaitar hare-haren da ke gudana a jihar Zamfara, wadda ke makwabtaka da Katsina.
Ya bayyana cewa matsalar tsaro ta fi karfin gwamnatin jihar Katsina kadai, don haka ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta shigo cikin lamarin domin kawo karshen ta’addanci a yankin.