An sanar da ranar fara duban watan Sallar Bana

0 80

Kwamitin koli kan harkokin addinin musulunci ya bukaci musulmai a kasarnan da su fara duban sabon watan musulunci na Shawwal daga ranar Juma’a, 22 ga watan Mayu.

Kwamitin ya fadi haka cikin wata sanarwa da mataimakin Sakatare Janar na kwamitin, Salisu Shehu, ya fitar jiya Litinin a Abuja.

Salisu Shehu ya kuma taya musulmai murnar gudanar da azumin watan Ramadan na bana, inda yayi addu’ar Allah (SWT) ya bawa dukkan musulmai damar ganin wani watan na Ramadan cikin koshin lafiya.

Daga nan sai yayi kira ga musulmai a fadin kasarnan da su saurari sanarwar shugaba na kasa na kwamitin koli kan harkokin addinin musulunci, dangane da karshen azumin watan Ramadan na bana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: